26 Nuwamba 2020 - 12:56
Allah Ya Yi Wa Tsohon Firayi Ministan Sudan, Sadiq al-Mahdi Rasuwa Bayan Fama Da Cutar Korona

Rahotanni daga kasar Sudan sun bayyana cewar Allah Ya yi wa tsohon firayi ministan kasar, Sadiq al-Mahdi, rasuwa a daren jiya Laraba bayan yayi fama da cutar Korona.

ABNA24 : Rahotannin sun ce a kwanakin baya ne dai marigayi Sadiq al-Mahdi ya kamu da cutar COVID-19 din inda ya ci gaba da fama da cutar har zuwa lokacin da Allah Ya yi masa rasuwa a daren jiya Laraban yana da shekaru85 a duniya.

Marigayi Sadiq al-Mahdi wanda kuma shi ne shugaban jam’iyyar ‘Umma’ ta kasar Sudan din ya kasance shi ne zababben firayi minista na karshe na kasar Sudan din sannan kuma ya rike wannan matsayi na firayi ministan kasar Sudan din tun daga shekarar 1986 har zuwa shekarar 1989 lokacin da tsohon shugaban kasar Sudan din Umar Hasan al-Bashir ya kifar da gwamnatinsa cikin wani juyin mulkin soji da ya jagoranta, inda tun daga nan ne ya soke matsayin firayi minista a kasar.

Jam’iyyar ‘Umma’ da marigayi Sadiq al-Mahdi ke wa jagoranci ita ce dai babbar jam’iyyar adawa ta kasar Sudan din kuma ta kasance a kan gaba wajen adawa mai tsanani da kokarin kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila.

342/